✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohuwar matar Adam A. Zango ta dawo harkar fim

Tsohuwar jarumar ta dawo bayan shafe shekara 13 da barinta masana'antar.

Bayan shafe shekara 13 da barin masana’antar Kannywood, Amina Uba Hassan, tsohuwar matar jarumi Adam A. Zango ta sake dawowa harkar fim.

Amina, wadda aka fi sani da Maman Haidar, ta fara fitowa a fina-finai tun farkon shekara ta 2000, kafin daga bisani ta auri Adam A. Zango a 2007.

Ta haifi danta namiji a 2008, amma wata biyar bayan haihuwar auren nata da Adam A. Zango ya mutu.

Bayan rabuwarsu, jarumarn ta ci gaba da harkar fim ba, sai a kwana nan ta fito a shiri mai dogon zango wanda kamfani 2Effects ya shirya, mai suna ‘Gidan Danja’.

“Yana da matukar wahala ga uwa kuma bazawara a ce bayan shafe shekaru masu yawa ka dawo yadda kake a masana’antar fim, na dauki tsawon lokaci ina shawara kafin na sake dawowa. Fitowa a fina-finai shi ne abin da na fi so, shi ya sa na dawo,” a cewarta.

Magoya baya sun jinjina mata kan irin rawar da ta taka a shirin da ake haskawa a tashar talabijin ta Arewa24.

%d bloggers like this: