Tsohuwar Kwamishinar Lafiya ta Jihar Bauchi, Dakta Zuwaira Hassan Ibrahim, ta rasu a wani hatsarin mota da ya ritsa da ita a kan titin Jos zuwa Bauchi.
Marigayiyar ita ce Shugabar Sashen Magunguna na Asibitin Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
- Mutum 18 sun mutu a nutsewar kwalekwale a Bauchi
- Shugabanni su ji tsoron Allah —Shaikh Dahiru Bauchi
- Zazzabi ya kashe mutum 8 a Bauchi
- Gwamnatin Bauchi ta bankado ma’aikatan bogi 2,116
‘Yan uwanta sun tabbatar wa da Aminiya cewa hadarin ya faru ne yankin Zaranda Gari a ranar Litinin da safe.
Ta fara aiki a asibitin a ranar 1 ga watan Nuwambar 2020.
Dakta Zuwaira ta yi Kwamishinar Lafiya ne karkashin mulkin tsohon gwamnan jihar, Barista Mohammed Abdullahi Abubakar.
Za a kuma jana’izarta a masallacin juma’a na asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa, da ke Bauchi.
Dakta Zuwaira ta rasu ta bar mijinta da ‘ya’ya uku.
Wakilinmu bai samu tattaunawa da babban Daraktan asibitin na ATBU-TH, saboda rashin daga wayarsa da ya yi.