✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohuwa daya kadai aka iske a Damasak bayan kwato shi daga Boko Haram

Wata tsohuwa daya kacal aka iske a garin Damasak, hedkwatar karamar Hukumar Mobar da ke Jihar Borno, bayan da aka kwato shi kwanakin baya daga…

Wata tsohuwa daya kacal aka iske a garin Damasak, hedkwatar karamar Hukumar Mobar da ke Jihar Borno, bayan da aka kwato shi kwanakin baya daga ’yan Boko Haram. Matar mai suna Yaa Sun, mai shekara 73 ta zauna a karkashin ’yan Boko Haram din kuma ta ce ba ta son barin garin. Wakilinmu wanda ya ziyarci garin a makon jiya ya ruwaito cewa, an kwato Damasak daga Boko Haram ne a ranar 30 ga Yulin bana, kuma babu kowa a garin, sai matar ce kawai a wani karamin dakinta na laka da ciyawa ta lullube. Ta ce duk da cewa akwai wuraren da za ta gudu, ta zabi ta zauna ne a Damasak saboda sojoji suna ba ta abinci da ruwan sha da kula da lafiyarta. “Ko lokacin da wadancan yara (’yan Boko Haram) suke nan babu abin da ya same ni, to yanzu babu abin da zai sanya in fice daga gidana,” inji ta. Tsohuwar wadda take magana da da Ingilishi kadan-kadan da kuma Hausa ta ce yanzu zaman lafiya ya fara dawowa a Damasak, inda ta ce za ta iya zuwa Legas in da ta zabi gudu daga garin, amma sai ta zauna abin ta. Kwamandan Bataliya ta 145 na sojin Najeriya da ke Damasak Laftana Kanar Mustapha Jimoh, ya ce lokacin da aka sake kwato garin wannan tsohuwar kadai aka iske a garin.