✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohuwa da jikokinta sun rasu bayan cin tuwon amala

Wata dattiuwa da danta da jikokinta sun rasu bayan sun ci tuwon amala a yankin Ilori na Jihar Kwara

Wata dattiuwa da danta da kuma jikokinta sun rasu bayan sun ci wani tuwon amala da ake zargin guba a ciki a Ilori, babban birnin Jihar Kwara.

Dattijuwar da iyalanta sun gamu da wannan jarabawa ne a yankin Eruda, kafin a garzaya da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilori, inda rai ya yi halinsa a ranar Talata.

Ma’aikatar lafiya jihar ta sanar cewa wasu mutum hudu da suka ci amalan da ake zargi suna farfadaow a asibitin.

Kwamishinar ma’aikatar, Dokta Amina El-Imam, “Muna yin iya kokarinmu, kuma muna kyautata zaton nan ba da jimawa ba za a sallame su.

“Mun kuma lura da cewa mazauna unguwar da abin ya faru ba sa kula da tsaftar muhalli yadda ya kamata.

“Abin da ya same su ba komai ba ne illa gubar abinci sakamakon yadda aka sarrafa rogon da aka yi garin amalan da shi.”

Kwamishinar ma’aikatar, Dokta Amina El-Imam, ta ce akwai wani mutun guda ya rasu a garin Osin Gada, da ke Karamar Hukumar Ilorin ta yamma sakamakon fama da ciwon ciki.

A cewar kwamishinar, ana zargin Lafun a cikin garim rogon da aka yi amalan da ya yi sanadiyyar rasuwar mutanen.

Dokta Amina ta ce wadanda suka ci amalan da babu Lafuna a cikin garin da aka yi amfani, babu abin da ya same su.

Kwamishinar ta ce wadanda suka harbu, musamman kananan yara, sun rika amai da gudawa, inda aka samu asarar rai.