✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon zakaran duniya a tseren gudu ya mutu

Kafin rasuwar Abdalelah Haroun, ya lashe kyaututtuka da yawa.

Tsohon gwarzon tsere na duniya, Abdalelah Haroun, dan Kasar Sudan da ya wakilci kasarsa a Qatar, ya mutu a hatsarin mota.

Hukumar kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ce ta sanar da rasuwar tsohon zakaran mai shekara 24 a ranar Asabar.

  1. Za a kara kudin burodi a Kano
  2. ’Yan dakon makaman yan bindiga sun shiga hannu

Haroun wanda ya kasance tsohon zakara a duniya a kan gudun mita 400, ya lashe kyautar zinare a gasar wasannin Asiya ta 2018 da kuma gasar wasannin motsa jiki ta Asiya ta 2015.

Baya ga azurfar da ya lashe a wasannin motsa jiki ta cikin gida a cikin 2016, mamacin ya samu kyautar tagulla a Gasar Zakarun Duniya ta 2017 da aka gudanar Landan.

Haroun ya samu cancantar zuwa  kasar Qatar ne a shekarar 2015 kuma yana daya daga cikin ’yan wasan da suka wakilci nahiyar Afirka.