✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban ’Yan Sanda Alkali Ya Gina wa Al’umma Masallacin Juma’a

Tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali  ya b da gudunmuwar masallacin Juma’a da ya gina a unguwar G.R.A Damaturu, Jihar Yobe.

Tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali  ya bayar da gudunmuwar masallacin Juma’a da ya gina ga mazauna Unguwar G.R.A Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

Alkali ya ce hakan ya yi daidai da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da ke cewa “Duk wanda ya gina masallaci, Allah Zai saka masa da gida a aljanna”.

Ya ce masallacin zai ba wa Musulmi damar zuwa su bauta wa Allah (SWA) cikin sauki da natsuwa.

Tsohon shugaban ’yan sandan ya ce ana iya gudanar da ayyukan ibada da da ma aure da sauransu a masallaci.

“Masallacin ba wai na sallah ne kawai ba, zai kunshi karantarwa da koyon addinin Musulunci,” in ji Alkali.

Ya kara da cewa an kafa kwamitin da zai kula da masallacin ta da jin dadin limamai da malamai da sauran masu kula da masallacin.

“Saboda haka, mun samar da wata kyauta ta musamman don mutanen da za su ba da gudummawa dangane tafiyar da wannan masallaci.”

Ya kuma ce za a gina makarantar Islamiyya a kusa da masallacin don koyar da ilimin musulunci ga yara maza da mata hade da manya.