✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon shugaban PDP da wasu sun koma APC a Yobe

Tsohon shugaban jam’iyyar adawa ta PDP Lawan Gana Karasuwa da wata tsohuwar ‘yar takarar Sanata Dakta Mairo Amshi  tare da wasu mabiyan jam`iyyar sun fice…

Tsohon shugaban jam’iyyar adawa ta PDP Lawan Gana Karasuwa da wata tsohuwar ‘yar takarar Sanata Dakta Mairo Amshi  tare da wasu mabiyan jam`iyyar sun fice daga jam’iyyar sun koma APC a jihar Yobe.

Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ne ya karbi sababbin ‘yan jam’iyyar a jiya Talata yayin kamfen da gwamnan ya jagoranta a birnin Gashuwa da ke Yobe ta Arewa.

A jawabin tsohon shugaban PDP da ya koma APC ya ce, ya yanke shawarar koma wa jam’iyyar mai mulki ne ta APC ganin irin ci gaban da jam’iyyar ta samar a wannan gwamnati a duk fadin kasar.