Tsohon shugaban kasar Mali, Moussa Traore, ya rasu a gidansa da ke Bamako, babban birnin kasar, yana da shekaru 83 a duniya.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito, iyalan marigayin sun ce ya rasu ne ranar Talata 15 ga watan Satumba.
- Takaitaccen tarihin Sarkin Biu Marigayi Mustapha Aliyu
- Masu garkuwa sun kashe jami’in DSS a Jihar Katsina
Moussa Traore ya mulki kasar ta Mali har tsawon shekaru 22, wato daga shekarar 1968 zuwa 1991 bayan da ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Moddibo Keita, shugaban kasar na farko bayan samun ‘yancin kai,.
Ya ci gaba da zama uban kasa da ake girmamawa, mai bai wa ‘yan siyasa shawara bayan da soji suka hambarar da gwamnatinsa a shekarar 1991.