✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban Kasa, Ernest Shonekan, ya rasu

Ya rasu a Legas, yana da shekara 85.

Tsohon Shugaban Najeriya na rikon kwarya,  Cif Ernest Shonekan, ya rasu.

Ya rasu ranar Talata a Legas yana da shekara 85.

Marigayin dai ya shugabanci Najeriya ne a matsayin Shugaban Kasa na rikon kwarya tsakanin ranar 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993.

Tsohon Shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha ne ya hambarar da gwamnatinsa yayin wani juyin mulki.