Tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Ibrahim Lamorde ya riga mu gidan gaskiya.
Lamorde ya rasu ne a birnin Cairo a ƙasar Masar inda ya je jinya kamar yadda aka sanar da safiyar yau Lahadi 26 ga watan Mayu.
- Yadda ta’addanci da talauci suke dabaibayi ga mazauna iyakar Nijeriya da Nijar
- Shugaban Burkina Faso ya tsawaita wa’adin miƙa mulki zuwa shekara 5
Lamorde wanda ya rasu yana da shekaru 61, ya riƙe shugabancin Hukumar EFCC daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Da farko dai an soma naɗa Lamorde daraktan ɓangaren ayyuka na EFCC lokacin da aka ƙirƙiro ta EFCC hukumar a shekarar 2003.
A watan Nuwambar 2011 kuma aka naɗa Lamorde a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na Hukumar EFCC a zamanin mulkin Goodluck Jonathan.
Daga bisani an tabbatar da Lamorde a matsayin shugaban hukumar a watan Fabarairun 2012 har zuwa 9 ga watan Nuwambar 2015.
Bayan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi nasarar lashe zaɓe a 2015, ya cire Lamorde tare da sauya shi da Ibrahim Magu a matsayin shugaban rikon ƙwarya na hukumar.
An haifi Lamorde a ranar 20 ga watan Disambar shekarar 1962 a jihar Adamawa inda ya shiga aikin ɗan sanda a shekarar 1986.