Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya jinjinawa Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje, dangane da dakatarwar da ya yi wa Sheikh Abduljabbar daga yin wa’azi.
Sanusi ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, bayan kammala jawabi a Landan, inda ya ce Kano tana nan a kan koyarwar Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo, kuma ba za su lamunci wani sabon abu daga wajen wani ba.
- Matakin Gwamnatin Kano kan Sheikh Abdujabbar ya yi daidai —JNI
- Za mu shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da Malamai — Ganduje
- Kwamandan ’yan bindiga Daudawa ya mika wuya a Zamfara
- An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya
“Kano ta jima a kan koyarwar Shehu Usman Danfodiyo kuma mu da muke yanzu zamu tabbatar da hakan ta dore, ba zamu lamunci wani ya zo mana da wani abu na daban ba.
“Hukuncin da gwamna ya dauka abun a yaba masa ne, kuma muna goyon bayansa a kan hakan,” a cewar Sanusi.
Tsohon Sarkin ya yaba wa malaman Kano kan yadda suka hade kai tare wajen bai wa gwamnati shawarar da ta dace.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Kano ta dakatar da Sheikh Abduljabbar daga yin duk wani abu da ya shafi wa’azi a fadin jihar, kan zarginsa da yin batanci ga sahabban Manzon Allah (S.A.W).
Kazalika, gwamnatin ta ba da umarnin rufe dukkanin majalisin da malamin ke karatu a fadin jihar.
Sai dai bayan martanin da Sheikh Abduljabbar ya yi na cewa gwamnatin jihar ba ta ba da damar yin muhawara da sauran malamai kan kalaman nasa ba.
Daga bisani Ganduje ya kafa kwamiti tare da ba da damar a shirya muhawara tsakanin Abduljabbar da malamai domin a yi baje koli na dalili a bainar jama’a.