A ranar Talatar da ta gabata ce aka yi wani mummunan hadarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya, inda mutum hudu suka kone kurmus ciki har da tsohon Sakataren Kungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Kaduna, Mista Dominic Uzu wadda tsohon ma’aikacin jaridar New Nigerian ne.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura a Shiyyar Zariya Alhaji Abubakar Murabus Tata ya shaida wa Aminiya cewa, “Da misalin karfe 12 na rana ne aka kira mu a waya cewa an yi hadarin a kauyen Dumbin Rauga kilomita shida daga Zariya a kan hayar Kaduna, inda muka nufi wajen sai muka ga motoci biyu ne suka yi hadarin da babbar mota da wata Toyota bas suna cin wuta. Fasinjoji goma ke cikin bas din ita kuma tirelar mutum uku, kuma duka motocin sun kama da wuta babu wanda zai iya zuwa wurin. Nan da nan muka sanar da jami’an kashe gobara cewa su kawo dauki, ba tare da bata lokaci ba suka iso a amma kafin su zo mutanen da ke motar fasinja su hudu sun kone kurmus, har daya daga cikinsu saboda konewa mu ne muka yi jana’izarsa, sai mutum shida mun kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello.”
Kwamandan ya ce rashin hakuri ne ya haifar hadarin duk da gyaran hanyar da ake yi, wanda ya sa yanzu hannu daya ake amfani da shi amma mutane suna son gaggawa.