✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina ya rasu

Marigayi Isah Katsina ya rasu yana da shekara 81 bayan fama da rashin lafiya.

Allah Ya yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Isah Katsina rasuwa.

Ya rasu a ranar Talata a asibiti sakamakon gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 81, kuma tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

An binne marigayi Isah Katsina a Makabartar Rimin Badawa, kuma ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya 14.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, Mataimakinsa, Mannir Yakubu da Shguaban Majalisar Jihar, Tasiu Musa Maigari na daga cikin wadanda suka halarci jana’izar.

Marigayi Isah Katsina yana daga cikin hazikan daliban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), da ke Zariya wanda suka kammala karatu a 1975.

Iyalansa sun shaida wa Aminiya cewa ya rike mukamin Sakataren Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya shiyyar Arewa ta tsakiya, sannan ya yi Shugaban Ma’aikatan Jihar Kaduna a zamanin mulkin Muhammad Lawan Kaita.

Ya rike mukamin Sakataren Gwamnatin Kaduna lokacin mulkin soji na Usman Mu’azu a 1984 sannan a daga 2000 zuwa 2003 ya rike mukamin a Jihar Katsina, karkashin mulkin marigayi Umaru Musa Yar’Adua.