Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Borno, Alhaji Usman Jidda Shuwa, ya riga mu gidan gaskiya.
Har ya zuwa ranar 28 ga watan Mayun wannan shekara, Alhaji Shuwa shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar Borno a wa’adin mulkin Gwamna Babagana Umara Zulum na farko.
- Abin da ya kamata Tinubu ya yi kafin cire tallafin man fetur —Atiku
- Bala Mohammed ya zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP
Wakilinmu ya ruwaito cewa, da Yammacin wannan Asabar Alhaji Jidda Shuwa ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri bayan ’yar takaitacciyar jinya kamar yadda makusantansa suka tabbatar.
Tarihi ba zai manta da Alhaji Jidda Shuwa ba wanda zakakurin jami’in kula da harkokin gudanarwa ne wanda ya shafe shekara da shekaru a matakin jiha da kuma tarayya.
Alhaji Jidda Shuwa wanda aka haifa a shekarar 1958, ya rasu bayan shafe shekaru 65 a doron kasa.
Nan da zuwa wani lokaci Gwamnatin Jihar Borno za ta sanar da bayanai game da yadda jana’izarsa za ta kasance.