✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Ministan Kudi Sonny Chu Okongwu ya rasu

Tsohon ministan ya rasu ne a ranar Laraba yana da shekara 87 a duniya.

Tsohon Ministan Kudi Sonny Chu Okongwu ya rasu a ranar Laraba, yana da shekara 87 a duniya.

Okongwu wanda masanin tattalin arziki ne, an haife shi nw a ranar 23 ga watan Satumba, 1934 a Karamar Hukumar Nnewi ta Jihar Anambra.

Ya rike mukamin Ministan Tsare-tsare daga 1985 zuwa 1986 sannan ya rike mukamin Ministan Kudi daga 1986 zuwa 1990 a lokacin mulkin soji karkashin Janar Ibrahim Babangida.
Mista Okongwu ya halarci Jami’ar Boston da ke Massachusetts a kasar Amurka daga 1961 zuwa 1965 inda ya karanci fannin Tsimi da Tanadi.