✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon minista Taoheed Adedoja ya bayyana aniyarsa ta zama Shugaban PDP

Tsohon Ministan Wasanni Farfesa Taoheed Adedoja ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar shugaban jam’iyar PDP na kasa baki daya. Ya ce, idan Allah yasa…

Tsohon Ministan Wasanni Farfesa Taoheed Adedoja ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar shugaban jam’iyar PDP na kasa baki daya. Ya ce, idan Allah yasa yayi nasarar hayewa bisa wannan mukami to, zai dinke barakar da aka samu a tsakanin shugabannin jam’iyar a cikin kankanen lokaci. Tsohon ministan wanda ya taba neman tsayawa takarar kujerar Gwamnan Jihar Oyo a shekara ta 2011, ya ce, rashin adalci ne ya haifar da kauracewar da wasu mambobin jam’iyar suka yi.
“Akwai gwamnoni da ministoci da ‘yan majalisun dokoki na tarayya da jihohi da kusoshin jam’iya da ake ji da su da suka kauracewa PDP tare da dimbin magoya bayansu saboda rashin adalci. Abu na farko da zan fara mayar da hankali idan na kama ragamar shugabanci shi ne, tabbatar da adalci ga kowane sashe na kasa ba tare da amincewa da bangaranci da kabilanci da banbancin addini ba,” inji Farfesa Taoheed Adedoja, wanda ya fadi haka a lokacin da yake bayyana kansa a matsayin mai sha’awar zama shugaban jam’iyar PDP na kasa a gaban kusoshi da daruruwan magoya bayan jam’iyar da suka halarci taron amincewa da fitowar da yayi da aka yi a Sakatariyar jam’iyar ta Jihar Oyo dake Molete a birnin Ibadan.
Ya ce, yana ganin shi ne yafi kowa cancantar rike wannan mukami ne saboda a cewar sa “nid an asalin Ibadan ne da aka haife ni a birnin Kano ne da yin ayyuka a jihohin Jigawa da Borno da Yobe da Adamawa da Kaduna da wasu jihohi a sashen kudu maso kudu da manyan mukaman da na rike a baya wadanda sun ishe ni fahimtar muhimman abubuwa da suka shafi zamantakewar al’ummomin kasa da za su yi min jagoranci wajen hada kan ‘ya’yan jam’iyar PDP da zai kai mu ga nasara a zaben shekara ta 2019.”
Farfesa Taoheed Adedoja, wanda kwanan baya aka daura masa aure da diyar tsohon shugaban jam’iyar PDP na kasa, Alhaji Bamanga Tukur, ya nuna bakin cikinsa da irin matsayin da ma’aikata masu aiki a hedkwatar jam’iyar dake Wadata Plaza a Abuja suke ciki. Ya ce, zai yi duk abun da yake iyawa wajen ganin an dawo da adalci a cikin jam’iyar ta yadda za a fita hakkin kowane sashe na kasa.
Jiga jigan da suka halarci wajen taron sun hada da shugaban jam’iyar PDP na jihar oyo, Mista Yinka Taiwo da tsohon jagora a majalisar dattijai Sanata Teslim Folarin da tsohon ministan wutar lantarki Elder Wole Oyelese da tsohon sakataren jam’iyar na jihar oyo, Alhaji Bashir Akanbi da tsofaffin shugabannin majalisar dokoki ta jihar oyo Hon. Moroof Atilola da Mista Ashimiyu Alarape.