Tsohon Kwamishinan Ayyukan Jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, ya soki lamarin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan taka hoton Tsohon Gwamnan Jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso yayin wani gangamin karbar wasu ’yan siyasa zuwa jam’iyyar APC a jihar.
Tun a ranar Asabar ce wani hoton Gwamna Ganduje yana tsaye da kafarsa a kan hoton Kwankwaso yayin gangamin ya karade kafafen sada zumunta.
- ’Yan Tijjaniya a Kudu sun yi wa Halifa Sanusi II mubaya’a
- Za mu yi maganin ’yan bindiga a Zamfara — Matawalle
Aminiya ta ruwaito cewa, wani rikici ya barke yayin babban gangamin jam’iyya mai mulki ta APC da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Kano.
Mu’azu wanda a yanzu ke zaman Shugaban Aikin Bututun NNPC-AKK da ake gudanarwa a jihar Kano, ya wallafa wani sako a shafinsa na Facebook inda ya yi kira ga Ganduje da cewa abin da ya yi bai dace ba.
Cikin dogon sakon da ya wallafa, Magaji ya ja hankalin Ganduje da cewar duk wanda suka ba shi shawarar aikata hakan ba su san siyasa ba.
Ya ce “Duk wanda ya ba da shawarar aikata haka tabbas bai san yadda siyasa take ba, ina mai baka hakuri ranka ya dade amma hakan bai dace daga wajen babba kamarka ba. …
“RMK (Rabi’u Musa Kwankwaso) ya kasance maigidanka a lokacin da ya yi Gwamnan Kano da kuma Ministan Tsaro.
“Wannan ba abin da ya dace ba ne kuma tabbas zai dawo mana a lokacin da ba yi aune ba.
“Ranka ya dade kana zagaye da mutane wanda ba nagari ba wanda ina da tabbacin da kai ne haka ke faruwa da kai da babu wanda zai zauna tare da kai…”
Tuni dai lamarin ya yamutsa hazo a jihar, inda mutane da dama ke Allah wadai da abin da Gwamnan ya yi a lokacin gangamin siyasar a ranar Asabar.