✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Kansila ya doke Mai Ladabtarwa A Majalisar Tarayya

Farfesa Benjamin Kumai Gugong na jam'iyyar APC ne yazo na uku da kuri'a 9,919

Mai Ladabtarwar Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai, Gideon Lucas Gwani, ya sha kaye a hannun dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar LP, Mathew Donatus don wakiltar mazabar Kkaramar Hukumar Kaura a majalisar.

Wanda ya ce zaben tsohon dan acaba ne kuma tsohon kansila ne a gundumar Kadarko da ke  Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna.

Yayin da yake bayyana sakamakon zaben a Hedikwatar Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna, Baturen Zabe, Farfesa Elija D. Ella, ya bayyana Donatus a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’a 10,508.

Gideon Lucas Gwani na jam’iyyar PDP wanda yake neman kujerar a karo na biyar ya zo na biyu ne da kuri’a 10,297 a wani gagarumin sauyin da ake kira ‘Guguwar Labour’ a Kudancin Kaduna.

Farfesa Benjamin Kumai Gugong na jam’iyyar APC ne yazo na uku da kuri’a 9,919.