Tsohon mai ba tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya samu sabon mukami da kamfanin jaridar The Sun.
Adesina, wanda ya kwashe shekara takwas a gwamnatin Buhari dai zai fara aiki ne a matsayin shugaban kamfanin, daga ranar daya ga watan Satumba mai zuwa.
Tsohon Kakakin, wanda a baya ya rike mukaman Editan Gudanarwa da kuma Babban Editan jaridar, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawarsa da kafar yada labarai ta The Crest, ranar Laraba.
Mamallakin kamfanin, Sanata Orji Uzor Kalu dai ya amince da nadin nasa.
Femi Adesina dai ya ce ko a lokacin da ya yi yunkurin barin aikinsa da jaridar a baya, sai Sanata Kalu ya shawarce shi da kada ya ajiye aikin gaba daya, ta yadda duk lokacin da ya kammala aikinsa ko kuma ba ya jin dadin gwamnatin, zai iya komawa.
“Na zo daga jaridar The Sun. A da ni ne Manajan Darakta kuma Babban Editan kamfanin. Lokacin da zan tafi sai Sanata Orji Kalu ya ba ni shawarar kada na ajiya aikin gaba daya, ta yadda duk lokacin da nake so zan iya dawowa ko da bayan shekara takwas, sannan ya yi alkawarin ba ni matsayin Shugaban kamfanin. Ba wai kawai da baki ya fadi hakan ba, sai da ma ya ba ni takardar aikin, har yanzu kuma ina da ita,” in ji shi a cikin tattaunawar.
Har ila yau, kafin nadin nasa da Buhari ya yi a 2015, shi ne Shugaban Kungiyar Editoci ta Najeriya (NGE).