✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPC ya kara farashin litar man fetur

Kamfanin mai na kasa NNPCL ya tabbatar cewa ya fara farashin litar man fetur zuwa N540

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya tabbatar da karin farashin litar man fetur a gidajen mansa da ke fadin Najeriya.

Aminiya a zaga gidajen mai a Kano inda ta iske gidan man NNPC da ke titin Club Road na sayar da litar fetur a kan N540.

“NNPC Limited na sanar a abokan hularsa cew ya kara farashin man fetur da duk gidajen mansa da ke fadin Najeriya, sakamakon sauye-sauyen da aka samu a yanayin kasuwa.

“Duk da cewa muna kokarin samar da kyawawan ayyuka da ganin cewa ba a rasa man ba, amma dole ba za a rasa sauyin farashi ba saboda dalilai na kasuwanci.