✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Jakadan Najeriya a Amurka ya rasu

Marigayi Adamu ya rasu ya bar mata da yara biyar maza biyu, mata uku.

Tsohon Jakadan Najeriya a kasar Amurka, Ingila da Switzerland, Adamu Muhammad ya rasu yana da shekara 83.

Dan uwan marigayin, Haruna Alhaji Muhammad ne ya shaida wa Aminiya rasuwar, yana mai cewa Ambasada Adamu ya rasu ne a ranar Alhamis da safe a Kaduna bayan ya yi fama da jinya,

Tuni dai aka yi wa marigaryin Sallar Jana’iza a Masallacin Juma’a na Yahaya Road da ke Unguwar Rimi GRA Kaduna da misalin karfe 1 na rana.

Alhaji Haruna ya ce marigayin ya yi aiki tare da kusan dukkan tsoffin shugabannin soja, sannan ya yi ritaya a lokacin tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami Abubakar a matsayin Mashawarci a Kan  Yaki Miyagun Kwayoyi da Laifukan da suka shafi Kudi.

Marigayi Adamu ya kasance jakadan Najeriya a Senegal sannan kuma ya yi aiki a Majalisar Dinkin Duniya.

Ya kasance mutum ne mai gaskiya da rikon amana, a tsawon lokacin da ya shafe yana hidimta wa kasarsa.

Marigayi Adamu ya rasu ya bar mace daya da yara biyar maza biyu, mata uku.

Tuni aka binne shi a Makabartar Unguwar Sarki, Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.