Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu.
Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
- Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4
- Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji
Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar.
Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da gidan Galadiman Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhininsa kan rasuwar Galadanci, tare da bayyana irin rawar da ya taka a gwamnatinsa.
“Rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci babban rashi ne ga gwamnatina da Jihar Kano baki ɗaya.
“Za a yi rashinsa saboda jajircewarsa da ƙwazon da ya nuna wajen inganta harkokin sadarwarmu,” in ji gwamnan.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, ’yan uwa da abokan arziƙi.