Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Sakkwato a jamhuriya ta biyu, Dokta Garba Nadama, ya rasu yana da shekara 82 a duniya.
Ya yi mulkin jihar ne dai a matsayin gwamna daga watan Janairun 1982 zuwa watan Nuwamban 1983 bayan rasuwar gwamnan jihar na farko zabebbe, wato marigayi Alhaji Shehu Kangiwa.
Ya yi karatun digirinsa na uku a fannin tarihi a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.
Ya rasu ya bar matan aure uku da ‘ya’ya da jikoki.
Iyalan marigayin sun tabatar da rasuwar ga Aminiya.