✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon gwamnan Ogun bai bamu bindigar AK 47 guda dubu ba- ‘Yan sanda

Hukumar ‘yan sanda a jihar Ogun ta karyata labarin da jaridar Premiums Times ta buga inda ta bayyana cewa, tsohon gwamnan jihar Ogun Sanata Ibikunle…

Hukumar ‘yan sanda a jihar Ogun ta karyata labarin da jaridar Premiums Times ta buga inda ta bayyana cewa, tsohon gwamnan jihar Ogun Sanata Ibikunle Amusu, ya mika wa rundunar ‘yan sanda tarin makaman da ya tanada kafin zaben da ya gabata cikin su harda bindigar AK 47 guda dubu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Abimbola Oyeyemi ya aike wa Aminiya ya shaida cewa a ranar 28 ga watan Mayu tsohon Gwamnan ya gayyaci Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun Bashir Makama inda ya damka masa motar silke ta APC guda daya da harsashen bindiga guda miliyan daya da dubu dari 440 da dari 420 da rigar silke guda 271 da hular kwano guda uku.

“Babu bindigar AK 47 ko kwara daya a cikin makaman da aka bamu, Gwamnan ya dai ambaci bindigar AK 47 guda dubu daya da gwamnatin jihar ta sayawa rundunar ‘yan sandan a shekarar 2012, don haka abin mamaki ne labarin da Jaridar Premiums Times ta buga”.Ya ce, rundunar ‘yan sandan jihar ta shigar da bayanan daukacin makaman zuwa ga babban ofishin rundunar ta kasa da ke Abuja.

Tun a ranar da tsohon gwamnan ya mika makaman ga hukumar ‘yan sandan wakilin Aminiya ya nemi bin bahasi inda a wanccan lokacin kakakin hukumar ‘yan sandan ya ce suna kan kirga makaman.