✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Gwamnan Kano Hamza Abdullahi ya rasu

A shekaranjiya Laraba ce Allah Ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ayyuka kuma Ministan Abuja Iya Mashal Hamza Abdullahi rasuwa. Iya Mashal…

A shekaranjiya Laraba ce Allah Ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ayyuka kuma Ministan Abuja Iya Mashal Hamza Abdullahi rasuwa.

Iya Mashal Hamza Abdullahi ya rasu ne a wani asibiti da ke kasar Jamus kamar yadda Fadar Sarkin Hadeja maihaifar marigayin ta bayyana.

Wata sanarwa da ta fito daga fadar ta ce “Innalillahi wa inna’ilahir raju’un. Muna bakin cikin sanar da rasuwar Iya Bayis Mashal Hamza Abdullahi, wanda ya rasu a Kasar Jamus. Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya jikansa da rahama Ya haskaka makwancinsa Ya YI masa sakayya da Aljannah.”

Marigayin wanda ya yi Gwamnan soja a tohuwar Jihar Kano a zamanin mulkin Janar Buhari a  1984, bayan da aka yi  wa Buhari juyin mulki, Janar Babangida ya nada shi Ministan Ayyuka daga baya ya nada shi Ministan Birnin Tarayya Abuja, daga bisani ya yi ritaya ya shiga harkokin kasuwanci.

Marigayin yana cikin manyan aminan Mai martaba Sarkin Hadeja, Alhaji Abubakar Maje. Ya rasu yana da shekara 75, ya kuma bar mata uku da ’ya’ya da dama.

Da yake bayani a kan marigayin, wani dan uwan  Sarkin Hadeja, Alhaji Maina Kawu Hadeja ya danganta rashin Hamza Abdullahi da babban rashi ga al’ummar Hadeja da Jihar Jigawa da kasa baki daya.

Ya ce Hamza Abdullahi  mutum ne mai halin kirki da kaunar Hadeja sannan mai kishin Arewa da zai yi wahala a maye gurbinsa. Ya bayyana marigayin da cewa ko a soja gwarzo ne da Najeriya ke alfahari da shi.

Hamza Abdullahi ya samu horo daga Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Yaki da ke Jamus a 1966, ya kuma yi karatu Cibiyar Soji ta Royal da ke Chichester a kasar Ingila a 1974. Sannan shi ne wanda ya kammala aikin rukunin farko (Phase I) na ginin Babban Birnin Tarayya Abuja, gabanin dawo da fadar kasar nan a lokacin Janar Babangida.