Tsohon gwamnan jihar Kano na mulkin soja, Iya Bayis Mashal Hamza Abdullahi mai ritaya, ya rasu a Jamus.
A cewar shafin tiwita na masarautar Hadeja na cewa, Hamza Abdullahi ya rasu a jiya Laraba a kasar Jamus.
Hamza shi ne tsohon Gwamnan Kano daga Janairu 1984 zuwa Agusta 1985 lokacin mulkin Janar Muhammadu Buhari.
Marigayin dan asalin jihar Jigawa ne a yanzu bayan cire jihar daga yankin jihar Kano.
Allah Ya ji kanshi da rahama Amin.