Tsohon Firaministan Mali, Modibo Keïta, ya rasu a kasar Morocco inda ake jinyar sa.
Gwamnatin kasar Mali ta ce Mista Modibo Kéita ya rasu yana bayan shafe shekara 78 a ban kasa.
- Boko Haram ta kashe mutum 56 a Jamhuriyar Nijar
- Yadda na haihu a hannun ’yan bindiga —Mai jego
- ‘Na ga yadda ake horar da yara su zama ’yan bindiga’
- Dogo Gide: Mutumin da ya hallaka Buharin Daji
“Mun samu rahoton rasuwar tsohon Firaminista Modibo Kéita a safiyar yau (Asabsar),” inji sashin yada labarai na Ofishin Firaministan Mali.
Tsohon Shugaban Mali da aka hambarar da gwamnatinsa, Ibrahim Boubacar ya nada misata Kéita a mukamin Firaminista a ranar 8 ga Janairu, 2015.
Mista Kéita ne ya maye gurbin Moussa Mara bayan harin da ’yan tawaye suka kai wa sojojin kasar a yankin Kidal a ranar 14 ga watan Mayun sheakar.
Gabanin zamansa Firaminista a mulkin Boubacar Keita, a 2012 gwamantin tsohon Shugaba Alpha Omar Konaré na dana shi firaminista.