Gogaggen dan jarida kuma tsohon editan Sashen Hausa na BBC, Isa Abba Adamu ya rasu a ranar Lahadi bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Dan uwansa Malam Yusha’u Ibrahim, ya tabbatar wa Aminiya cewa Isa Abba ya rasu ne a Landan, kuma a can za a za a yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
- Ana Laluben Hanyar Sa Yara Miliyan 10 A Makaranta A Najeriya
- Kotu ta yanke wa dan Najeriya hukuncin rataya a Malaysia
An haifi marigayi Isa Abba Adamu ne a shekarar 1961 kuma ya kammala karatun digirinsa na farko a Jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 1985.
Tsohon ma’aikacin gidan talabijin na Jihar Kano (CTV) ne kafin ya koma Sashen Hausa na BBC.
Marigayin, ya rike mukamai da dama a BBC, tun daga matakin furodusa har zuwa edita.
Bayan ya yi murabus daga BBC, marigayi Isa Abba ya koma Cibiyar Nazarin Dokoki da ke Abuja, inda ya rike mukamin darakta, daga baya ya yi murabus ya sake komawa Landan.
Bayan nan ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada shi mamba na kwamitin amintattun Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN).
Marigayi Isa Abba Adamu ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya hudu.