✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC za ta lashe zaɓen Gwamnan Edo — Ganduje

Za mu ci gaba da aiki takuru domin mamaye duk yankunan Kudu maso Kudu a siyasance.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa na cewa jam’iyyar za ta lashe zaɓen gwamnan jihar Edo da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Ganduje ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa (NUJ) reshen jihar Kano ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Aminu Garko a ranar Alhamis.

Ya ce, an samar da tsare-tsaren siyasa domin share fagen samun gagarumin rinjaye na ɗan takarar jam’iyyar a yayin da suke shirin tukarar zaɓen da za a gudanar a watan Nuwamba.

Ganduje ya ce, “Na yi imanin yaƙin neman zaɓenmu yana cikin tsari, muna shirin tunkarar wannan zaɓe kuma mun yi imanin cewa za mu iya farfaɗo da jiharmu.

“Jiha ce ta jam’iyyar APC amma saboda wasu matsaloli na cikin gida mun rasa ta a hannun PDP amma muna da tabbacin za mu ƙwato jihar.

“Ondo, jiha ce ta jam’iyyar APC kuma a lokacin da tsohon Gwamnan ya rasu ya bar matsaloli da dama, amma mun samu nasarar magance waɗannan matsalolin.

“Mun gudanar da zaɓen fidda gwani, mun yi nasarar samun wanda suke so.”

Ganduje ya ce, “Idan muka yi nasara a Edo, za mu samu ƙarin jiha a jam’iyyar. Zai kasance jihohi 21 daga cikin 36 na APC ne.

“A shekarar baɗi, akwai Jihar Anambra, wadda ta kasance jihar da APGA ke mulki tsawon shekaru, amma mun ɓullo da wani sabon tsari.

“Shiyyoyin siyasar Arewa da Kudu-maso-Gabas duk suna iƙirarin cewa an mayar da su saniyar ware.

“Shiyyar yankin Kudu-maso-Gabas suna faɗin irin haka. Amma abin da muke gaya musu shi ne, su ne suka suka ƙirƙiri hakan.

“Ta yaya za ku sami jihohi biyar a ƙarƙashin jam’iyyun siyasa hudu? Me zai zama ribarku a siyasance?”

Ya ce jam’iyyar na aiki tuƙuru don ganin ta samu ƙarin jihohi daga shiyyar, yana mai cewa, “Muna so mu fara da Anambra.

“Tuni muna da Ebonyi da Imo. Yanzu muna kutsawa cikin wannan shiyya don tabbatar da cewa mun mamaye yawancin jihohin.