✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon dan wasan Barcelona, Maxi Rolon ya mutu a hatsarin mota

Matashin dan wasan ya mutu sakamakon hatsarin mota da ya yi a Ajentina.

Tsohon dan wasan Barcelona Maxi Rolon da ya buga wa kungiyar wasanni a rukuni matasa daga 2010 zuwa 2016, ya mutu a hatsarin mota a garin Rosario da ke kasar Argentina.

Lamarin ya faru ne yayin da motar dan wasan ta kwace masa ta daki bishiya, wanda a dalilin haka ya rasa ransa da tare da wani dan uwansa mai shekara 30.

Barcelona ta wallafa a shafinta na Twitter cewar “Muna bakin cikin sanar da mutuwar Maxi Rolon, dan wasan Barcelona a rukunin matasa, wanda ya buga wasanni daga 2010 zuwa 2016. Muna jajanta wa iyayensa da ‘yan uwansa.”

Barcelona ta dauki Rolon tun yana shekara 10 a duniya, inda ya ci gaba da murza leda har zuwa Janairun 2016, kafin ya warware kwantaraginsa da kungiyar.

Dan wasan gefen ya buga wa kungiyar Barcelona rukunin matasa wasanni da dama, wanda har ya lashe gasar Zakarun Turai na ‘yan kasa da shekara 19 da kungiyar.