✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan wasan A C Milan ya zama Magajin Gari

Tsohon dan wasan A C Milan Kakha Kaladze ya zama Magarin Garin Tbilisi bayan ya lashe zaben da ya gudana a babban birnin Tbilisi na…

Tsohon dan wasan A C Milan Kakha Kaladze ya zama Magarin Garin Tbilisi bayan ya lashe zaben da ya gudana a babban birnin Tbilisi na Gerogia.

Tsohon dan wasan, mai shekara 39, ya samu kashi 51 cikin kuri’un da aka kada a ranar Asabar da ta gabata.

Shi dai tsohon dan wasan, ya lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai sau biyu a cikin shekara 9 da ya yi yana taka leda a qungiyar. Sannan ya yi ritaya daga kwallo a shekarar 2012, inda ya koma harkar siyasa.

Kaladze ya rike mukamin Ministan Makamashi a Oktoban bara. Amma sai ya ajiye mukamin domin ya samu damar tsayawa takarar Magajin Garin na Tbilisi mai mutane kimanin Miliyan 1.2.