✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Alhaji Bashir Tofa, ya rasu

Za a yi jana’izarsa a gidansa da ke Gandun Albasa a Kano, da karfe 9:00 na safe.

Tsohon dan takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar NRC, Alhaji Bashir Usman Tofa, ya rasu.

A cewar wata majiya daga iyalansa, ya rasu ne bayan Sallar Asuba ranar Litinin, a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano bayan gajeruwar jinya.

Ko a ranar Juma’ar da ta gabata sai da aka yada jita-jitar cewa fitaccen dan siyasar, dan kasuwa kuma marubucin ya rasu, musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

Sai dai daga bisani iyalansa sun karyata labarin, inda suka ce yana dai kwance ne a asibitin, ba shi da lafiya.

Ya rasu yana da shekara 75 a duniya.

Daya daga cikin ’ya’yan marigayin, wacce kwana uku da suka wuce ta karyata labarin ce ta tabbatar da rasuwar da safiyar Litinin.

Za a yi jana’izar marigayin ne a gidansa da ke unguwar Gandun Albasa a birnin Kano, da misalin karfe 9:00 na safe.

Marigayin dai shi ne ya tsaya wa jam’iyyar NRC takarar Shugaban Kasa a shekarar 1993, inda ya fafata da marigayi MKO Abiola na SDP, kafin daga bisani a soke zaben.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Bashir Tofa, ya shahara wajen bayar da shawarwarin yadda za a magance matsalolin da ke addabar Najeriya.