Tsohon dan takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar NRC, Alhaji Bashir Usman Tofa, ya rasu.
A cewar wata majiya daga iyalansa, ya rasu ne bayan Sallar Asuba ranar Litinin, a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano bayan gajeruwar jinya.
- ‘Yadda nake kai ’ya’yana daji ’yan bindiga suna da lalata da su’
- ‘Daga yanzu duk wanda zai ziyarci Aso Rock sai an masa gwajin COVID-19’
Ko a ranar Juma’ar da ta gabata sai da aka yada jita-jitar cewa fitaccen dan siyasar, dan kasuwa kuma marubucin ya rasu, musamman a kafafen sada zumunta na zamani.
Sai dai daga bisani iyalansa sun karyata labarin, inda suka ce yana dai kwance ne a asibitin, ba shi da lafiya.
Ya rasu yana da shekara 75 a duniya.
Daya daga cikin ’ya’yan marigayin, wacce kwana uku da suka wuce ta karyata labarin ce ta tabbatar da rasuwar da safiyar Litinin.
Za a yi jana’izar marigayin ne a gidansa da ke unguwar Gandun Albasa a birnin Kano, da misalin karfe 9:00 na safe.
Marigayin dai shi ne ya tsaya wa jam’iyyar NRC takarar Shugaban Kasa a shekarar 1993, inda ya fafata da marigayi MKO Abiola na SDP, kafin daga bisani a soke zaben.
Kafin rasuwarsa, Alhaji Bashir Tofa, ya shahara wajen bayar da shawarwarin yadda za a magance matsalolin da ke addabar Najeriya.