✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan sanda ya kashe ’yan makaranta 24 a Thailand

Wani tsohon dan sanda ya kashe wasu yara ’yan makaranta 24 tare da jikkata wasu mutane 11 a wata makaranta a kasar Thailand

Wani tsohon dan sanda ya kashe wasu yara ’yan makaranta 24 tare da jikkata wasu mutane 11 a wata makaranta a kasar Thailand.

Tsohon dan sandan ya je makarantar kanana yaran ne a garin Uthai Sawan da ke Arewa maso Gabashin kasar a ranar Alhamis da tsakar rana dauke da bindiga, da kuma wuka a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Da shigarsa makarantar bai ga dansa ba, sai ya fito da wuka ya soma kisan mai uwa-da-wabi, inda ya soki da yara da yawa, da malamai, da kuma wadansu ma’ikata masu kula da yaran.

Sannan da ya koma gida ya hallaka dan nasa, da kuma matarsa, daga bisani kuma ya kashe kansa.

A cewar ’yan sanda, an kori mutumin daga aikin dan sanda ne a shekarar da ta wuce kuma a ranar da abin da ya faru, daga zaman kotu yake a inda ake sauraron shari’ar da ake yi masa na ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Cikin wadanda ya hallaka har da wata malama mai cikin watan takwas wanda ya soke ta da wuka, baya ga yara ’yan shekaru daya zuwa biyar su 24.