✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ɗan sandan ƙarya a Kano

Yana damfarar jama’a da shigar jami’an ‘yan sandan da kuma lalata martabar Rundunar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama Salisu Bala mai shekara 31, wanda ya daɗe yana karɓar kuɗi tare da addabar jama’a da sunan shi ɗan sanda ne.

A sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce ɗan sandan na bogi mazaunin unguwar Kurna Quarters ne a cikin birnin Kano.

Jami’an ‘yan sanda na musamman da ke Unguwar Koki Quarters a Kano ne suka bi sawu suka kama shi, inda aka gan shi, sanye da baƙar rigar ‘yan sanda mai ɗauke da hular kakin ‘yan sanda.

An ce ya damfari jama’a da ba su ji ba, ba su gani ba inda yake shigar jami’an ‘yan sandan da lalata martabar Rundunar.