✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan Majalisar Tarayya daga Kano ya rasu sanadiyyar COVID-19

Tsohon mamba a Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Fagge daga jihar Kano, Hon. Danlami Hamza ya rasu.

Tsohon mamba a Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Fagge daga jihar Kano, Hon. Danlami Hamza ya rasu.

Ya rasu da yammacin ranar Lahadi a cibiyar killace masu dauke da cutar Coronavirus ta Kwanar Dawaki a jihar Kano.

Tuni aka yi jana’izarsa cikin motar asibiti a unguwar su ta Fagge dake cikin birnin Kano.

Kafin rasuwar sa, ya taba zama dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Fagge daga shekarar 1999 zuwa 2011 karkashin tsohuwar Jam’iyyar ANPP.

Cincirindon mutane daga sassa da dama na Kano ne suka halarci jana’izar mamacin da aka yi da yammacin Lahadi.