Rahoton da kafar watsa labarai ta Naija news ta kalato ya ce tsohon dan kwallon Najeriya, Philip Osondu ya rasu. Ya rasu ne a ranar Juma’ar da ta wuce a wani asibiti da ke Beljiyam.
Rahoton ya ce Osondu da kansa ya je asibiti a ranar Alhamis don a duba lafiyarsa inda rai ya yi halinsa washegari.
Dan shekara 48 Osondu ya yi wa Najeriya kwallo a matakin matasa musamman a kungiyar kwallon kafa ta U-16 amma bai taba yi wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kwallo ba.
Ya taba lashe dan kwallon da ya fi nuna kwazo a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na ’yan kasa da shekara 16 da aka yi a Kanada a 1987 inda tsohuwar Tarayyar Sobiyet ta lallasa Najeriya a wasan karshe.
Ya taba yi wa kungiyar kwallon kafa ta Anderletch da ta RWDM dukkansu a Beljiyam kwallo daga nan ya yi ritaya. Bayan ya yi ritaya sai ya samu aiki a Beljiyam kuma ya ci gaba da zama a can kafin rai ya yi ha,linsa a ranar Juma’ar da ta wuce.
An haifi Osondu ne a garin Aba a 1971.
a Anderletch da ta RWDM kwallo daga nan ya yi ritaya. Bayan ya yi ritaya sai ya samu aiki a Beljiyam kuma ya ci gaba da zama a can kafin rai ya yi ha,linsa a ranar Juma’ar da ta wuce.
An haifi Osondu ne a garin Aba a shekarar 1971.