✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Kamaru ya rasu

Tsohon dan kwallon Kamaru wanda ya yi suna wajen yin keta a Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 1990 Benjamin Massing ya rasu.  Ya rasu…

Tsohon dan kwallon Kamaru wanda ya yi suna wajen yin keta a Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 1990 Benjamin Massing ya rasu.  Ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata yana da shekara 55. Akan tuna yadda Benjamin ne ya yi keta a wasan farko da Kamaru ta buga da Ajantina a gasar cin kofin duniya da aka yi a 1990 inda aka ba shi jan kati a wata keta da ya yi.

Bai sake buga wasa ba sai a wasan da Kamaru ta hadu da Ingila, inda a nan ma ketar da ya yi ne ta janyo aka ba Ingila bugun fanariti, da hakan ta sa Ingila ta doke Kamaru da ci 3-2.

Benjamin dai ya taba yi wa kulob din Creteil na Faransa wasa sannan ya buga wa Kamaru wasa sau 34 a tsakanin shekarar 1986 zuwa 1992.  Kawo yanzu ba a sanar da takamaiman abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa ba.