✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Chelsea ya rasu

A shekaranjiya Laraba ce aka sanar da rasuwar tsohon dan kwallon kulob din Chelsea da Manchester United da ke Ingila, Ray Wilkins.   Ray ya rasu…

A shekaranjiya Laraba ce aka sanar da rasuwar tsohon dan kwallon kulob din Chelsea da Manchester United da ke Ingila, Ray Wilkins.  

Ray ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan a lokacin da ya kusa cika shekara 52.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, tsohon dan kwallon ya rasu ne bayan ya kamu da cutar bugun zuciya da hakan ta sa aka garzaya da shi asibiti.

An ce tun da aka garzaya da Ray Wilkins asibiti a makon jiya bai san halin da yake ciki ba, hasali ma yana amfani da wata na’ura ce da aka dasa masa wajen yin numfashi.

Ray Wilkin yana daga cikin ’yan kwallon Manchester United da suka lashe kofin kalubale (FA) na Ingila a 1983 kimanin shekara 35 da suka gabata kafin daga bisani ya koma kulob din Chelsea.  Kuma ya yi kwallo ne a bangaren tsakiyar fili.