An cafke wani dan bindiga da ya ce ya tuba ya koma satar shanu da garkuwa da mutane.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ce ta sake kama tsohon dan bindigar ne tare da wasu abokan sana’ar sa biyu a Karamar Hukuamr Charanchi ta Jihar Katsina bayan sun yi fashin shanu.
- Matasa sun babbake wanda ya fille kan manomi
- Daukar makami don kare kai laifi ne —Babban Hafsan Soji
Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya ce bayan tuban dan bindigar, mai suna Abdullahi Mai-Rafi, ya fara aiki a karkashin ofishin mashawarcin gwamnan jihar kan harkokin tsaro.
SP Gambo Isah ya ce dubun mutum ukun ta cika ne bayan sun kai wa wani makiyayi hari ranar 11 ga August, 2021, a Dajin Dammarke a Karamar Hukumar Ingawa suka yi masa awon gaba da shanu 20 da kudinsu ya kai Naira miliyan 7.5.
Sun kuma kwace wa makiyayin tsabar kudi Naira 40,000 da wayoyin hannu guda hudu.
“Ranar 24 ga Agusta, 2021, da misalin 07.30 na safe, su ukun suka sake komawa gidan makiyayin za su kara yin awon gaba da wasu shanu 20 da tumaki, amma ’yan sanda suka ritsa su suka cafke su.
“A lokacin da ake bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma shugaban gungun, Abdullahi Mai-Rafi ya tabbatar cewa shi ne ya hada baki da wasu aka sayar da shanun satan a Kasuwar Dankama da eke Karamar Hukumar Kaita ta jihar.
“An kwato biyu daga cikin shanun da tsabar kudin N444,000 daga hannunsu a matsayin shaida.
“Abdullahi Mai-Rafi tsohon dan bindiga ne da ya tuba, har ya fara aiki a ofishin mai ba wa gwamna shawara kan harkokin tsaro,” inji shi.