Tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Victor Samuel Malu mai ritaya ya rasu yana dan shekaru 70 a duniya.
Malu ya rasu jiya a wani asibiti da ke birnin Kairo a cikin kasar Egypt.
Wata majiya da ke kusa da iyalansa ta shaidawa manema labarai a Makurdi cewa lamarin ya auku ne yayin da marigayi Malu ya tafi kasar Egypt don a duba lafiyarsa.
Marigayin shi ne tsohon shugaban rundunar sojojin Najeriya a zamanin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo tsakanin shekarar 1999 zuwa shekarar 2001. A baya ya taba rike mukamin babban kwamandan sojojin da ke tabbatar da zaman lafiya a kasar Laberiya tsakanin shekarar 1996 zuwa shekarar 1998.