✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsoho mai shekaru 68 ya yi wa ‘yarsa mai shekara 15 da kawayenta 2 fyade

Wani tsoho mai shekaru 68 mai suna Isa Showunmi da yi wa ‘yar cikinsa mai shekaru 15 da kawayenta 2 fyade ya shiga komar ‘yan sanda…

Wani tsoho mai shekaru 68 mai suna Isa Showunmi da yi wa ‘yar cikinsa mai shekaru 15 da kawayenta 2 fyade ya shiga komar ‘yan sanda a Legas. 

Mai magana da ‘yawun ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa, yarinyar wac

Faston da ake zargi da yi wa yar shekara 15 ciki.

ce aka sakaye sunanta ta shaida wa rundunar cewa mahaifin nata ya dade yana lalata da ita a cikin shekaru 3 da suka gabata, ta ce ya kuma yi lalata da kawayenta biyu da suka kai mata ziyara a gidan su da ke Imota a yankin Ikorodu”. Yarinyar ta ce, a baya bayan ma mahaifin nata ya yi mata fyade a ranar 23 ga watan jiya, kuma ya amsa laifin sa a lokacin da ake bincikar sa kuma yazu hakama an gurfanar da shi a gaban kotu”. In ji shi.

Haka zalika, rundunar ‘yan sandan ta Legas ta kuma kame wani fasto mai suna Pope Paul da ake zargi laifin yi wa yarinya ‘yar shekaru 15 ciki ta kuma kame wani dattijo mai suna Aliyu Muhammad shi ma akan zargin yin lalata da ‘yar shekaru 14 a wani kango wadanda dukkan su a ka gabatar da su a kotu.