Matar Shugaban Kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta ce masu kutse a intanet sun shiga shafinta na Instagram inda suka wallafa labarin karya da ke halasta ci gaba da amfani da tsoffin takardun N500 da N1000 zuwa 1 ga Mayu, 2023.
Aisha ta nesanta kanta da labarin, wanda ta ce aikin gurbatattun mutane ne da suka yi wa shafinta kustse tun a 2018 har zuwa bara.
- Mahara sun kona sakatariyar karamar hukuma a Kogi
- Batanci ga Annabi: Iran ta karrama matashin da ya kai wa Salman Rushdie hari
“Hankalina ya kai kan wani labarin karya da aka yada a shafina na Instagram wanda kuma ke hade da shafina na Facebook, kuma na ba da umarnin a cire labarin.
“Ko shakka babu wannan aikin wasu bata-gari ne da ke suka share wasu sakonnin da na wallafa tun a 2018 zuwa karshen shekarar bara inda na wallafa bidiyo da hoton lallen da na yi na ABAT a matsayin alama ta kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC bangaren mata…,” in ji Aisha.
Ta ce duk wanda ya aikata wannan, bata-gari ne mai muguwar zuciya wanda ke son yin amfani da shafukanta na sada zumunta wajen taba mutuncita.
“Amma ina mai tabbatar muku wannan shi zai zama na farko kuma na karshe da zan nesanta kaina da labarin karya a shafukana na sada zumunta,” in ji ta.
Ta ce domin cire wa mutane shakku, tuni CBN ya fito ya yi watsi da labarin, yana mai cewa ba gaskiya ba ne.
CBN ya sake jaddada cewa tsohuwar N200 kadai aka amince a ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga Afrilu kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wa ’yan kasa ran 16 ga Fabrairu, 2023.