Tsoffin kansiloli 69 da Sakatarorin Kananan Hukumomi 14 a Jihar Zamfara sun yi kaura daga jam’iyyar APC zuwa PDP mai mulkin jihar.
Gwamnan Jihar, Bello Muhammad Matawalle wanda ya karbe su da kansa ya bayyana farin cikinsa tare da kiransu su kasance masu kyakkyawar manufar ciyar da jihar gaba.
- Kwamishina ya kashe N25m wurin daukar nauyin auren zaurawa a Zamfara
- ’Yan bindiga sun sace ’yan sanda 12 a hanyar Zamfara-Katsina
Matawalle ya ce kofofinsa a bude suke ga kowa wajen hada kai tare da shi domin lalubo hanyoyin da suka dace don ci gaban jihar.
Kansiloli tsakanin shekarar 2012, 2015 zuwa 2019 ne suka sauya shekar karkashin inuwar Kungiyar Tsofaffin Kansiloli, reshen jihar ta Zamfara.
Jagoran kansilolin, Alhaji Tukur Muhammed Magami ya ce sun yanke shawarar barin tsohon mai gidan nasu ya biyo bayan imaninsu da salon shugabancin gwamnan, musamman wajen yaki da rashin tsaro da samar da kyakkyawan yanayin siyasa a jihar.
Kazalika, kakakin tsofaffin sakatarorin kananan hukumomi 14, Alhaji Sa’adu Mayana ya bayyana cewa Matawalle ya sauya jihar zuwa ga mataki na gaba.