✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsofaffin ’yan kungiyar Biyafar sun yaba wa Buhari

Jami’an ’yan sanda da suka tallafawa kungiyar Biyafara daga sashen gabashin kasar nan wadanda aka yi musu afuwa kuma aka yi musu ritaya daga rundunar…

Jami’an ’yan sanda da suka tallafawa kungiyar Biyafara daga sashen gabashin kasar nan wadanda aka yi musu afuwa kuma aka yi musu ritaya daga rundunar ’yan sandan Najeriya ta shirin afuwar shugaban kasa ta ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2000 lokacin mulkin shugaba Obasanjo wadanda kuma gwamnatin Buhari ta amince ta biya su hakkokinsu na fansho sun ce yaki ya kare har abada.
Sun yaba wa shugaba Muhammadu Buhari saboda amincewar da ya yi a biya su fanshonsu ba tare da wani bata lokaci ba.
Shugaban kungiyar ’yan sandan, Cif Mathew Udeh ya yaba wa shugaban kasa kan matakin da ya dauka tare da imani da hadewar kasar nan.