✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsofaffin Shugabannin Jami’o’i za su shiga tsakanin Gwamnati da ASUU

Yajin aikin ya shafi kusan dukkan al’ummar Najeriya.

Majalisar Tsofaffin Shugabannin Jami’o’in Najeriya (CVCNU) ta kafa kwamitin da zai sulhunta Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) kan yajin aikin da suke gudanarwa.

Tsohon Sakataren Majalisar, kuma guda daga jagororin tawagar sulhun, Farfesa Michael Faborode ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata a Abuja.

Ya ce babban burin kwamitin shi ne dakile tabarbarewar lamura a tattaunawar ASUU da gwamnati, lamarin da ya ce yajin aikin ya shafi da dama daga al’ummar Najeriya.

A cewarsa, samun biyan bukata a sulhun ya sanya babu kowanne shugaban jami’a mai ci a kwamitin, kuma duk mambobin tsoffin ma’aikata ne da aka tsamo sunayensu daga ma’adanar bayanai ta CVCNU.

“A matsayin mu na dattawa ba za mu nade hannayenmu muna kallo gininmu ya rushe ba, don haka mu ka ga dacewar daukar wannan mataki.

“Don haka duk abin da za a iya yi don cimma matsaya da sulhu tsakanin bangarorin biyu, ta hanyar amfani da shawarwarin kwamitin Farfesa Nimi Briggs za mu yi shi.

A cewarsa, yanzu haka suna kokarin isar da wannan sako ga Gwamnatin Tarayya da kuma kungiyar ASUU, don amincewa da shiga tsakanin kwamitin dattawan.

“Tawagar za ta tuntubi kwamitin Farfesa Nimi Briggs don fahimtar tushen matsalar, sannan su duba bangarorin da Gwamnatin Tarayya da kuma ASUU ke adawa da shi.

“Bayan haka, tawagar za ta lalubo hanyoyin warware bangarorin da ake takaddama a kai, tare da rarrashin kawo karshen matsalar cikin kwanciyar hankali.

“Za a fara tattaunawar ne ta yanar gizo (Zoom), daga nan ne idan an kai gabar da kowa ya gamsu sai a koma a zahiri.”

Tawagar ta hada da tsohon Shugaban Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) Farfesa Jibril Aminu, da tsohon Shugaban Jami’ar Ibadan (UI) Farfesa Olufemi Bamiro, da tsohon shugaban Jami’ar Calabar (UNICAL) Dokta Nkechi Nwagogu, da shugaban Kwalejin Kimiyya Farfesa Ekanem Braide.

Sauran sun hada da tsohon shugaban Jami’ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK) Farfesa Joe Ahaneku, da tsohuwar Shugabar Jami’ar Tarayya ta Dutse Farfesa Fatima Mukhtar, da tsohon shugaban Jami’ar Uyo (UNIUYO) Farfesa Akpan Ekpo da dama daga mambobin CVCNU.