✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsofaffin manyan Sojoji na zanga-zanga a Abuja

Sun ce duk zaman tattaunawa da suka yi da Ministan a kan batun amma ya yi kememe.

Wasu manyan hafsoshin sojojin da su ka yi riyata sun mamaye shalkwatar tsaro da ke Abuja suna zanga-zanga kan rashin biyansu alawus da sauran hakkokinsu.

Tsofaffin hafsoshin sojojin sun yi dandazo ne a kofar Shalkwatar tsaro duk da ruwan saman da ake yi a ranar Litinin don matsa wa ma’aikatar ta biya su hakkokinsu.

Tsofaffin hafsoshin sun rufe kofar shiga shalkwatar tsaron ta Ship House a inda suka hana shiga da fita cikin ginin, suna masu ikirarin sai an biya musu bukatunsu.

Hafsoshi Sojojin musu ritaya na zanga-zangar ne a karkashin kungiyarsu ta tsofaffin hafsoshin sojoji da kuma kungiyar gamayyar masu ruwa da tsaki a aikin soji musu ritaya.

Tsofaffin soji sun zargin Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya da nuna halin ko oho kan halin da suke ciki.

Mai magana da yawun masu zanga-zangar, Abiodun Durowiye-Herberts ya shaida wa manema labarai cewa, ba za su bar kofar Ma’aikatar Tsaron ba domin kuwa a nan za su kwana.

“Mun zo nan tare da mata da ‘ya ‘yanmu, da marayu, da kuma iyayen marayu wadanda mazajensu su ka mutu a wurin yakar ‘yan Boko Haram, ba kuma za mu bar nan ba, sai Magashi ya biya mu hakkinmu,” in ji Abiodun.

Kungiyoyin na zargin Ministan da kin biyansu ne duk da Shugaba Buhari ya bayar da izini a biya su.

Sun ce duk zaman tattaunawa da suka yi da Ministan a kan batun amma ya yi kememe.

Wakilinmu ya kira kakakin Ministan Tsaro Mohammed Abdulkadir don jin ta bakinsa, sai ya tura shi wurin Babban Sakataren Ma’aikatar, Ibrahim Kana.

Sai dai Babban Sakataren bai daukar wayar wakilinmu ba har lokacin hada wannan rahoto.

Ana iya tuna cewa, a watan Janairu tsofaffin sojojin suka yi irin wannan zaman dirshan kan hakkokinsu a Ma’aikatar Kudi da ta Tsaro, da kuma Majalisar Dokokin Tarayya.