Tsofaffin malaman makaranta sun gudanar da zanga-zanga a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom saboda kin biyansu hakkokinsu.
Masu zanga-zangar sun toshe babbar titin IBB da ke cikin birnin na Uyo na tsawon sama da sa’a guda tare da hana masu ababen hawa wucewa.
- Ruftawar gadar jirgin kasa ta yi ajalin mutum 23 a Mexico
- Mutum 5 sun kone kurmus a gobarar tankar mai a Ibadan
Suna dai kalubalantar gwamnati ne kan rashin biyansu hakkokinsu bayan kammala aiki tare da korafin a kara masu kudaden fansho.
Tsofaffin malaman sun kuma koka cewa ana biyan da dama daga cikinsu N2,000 ne kacal a matsayin fansho.
Sun rike kwalaye dauke da rubuce-rubuce suna rokon Gwamnan Jihar da ya ceto rayuwarsu daga cikin halin da suka shiga, inda suka ce da yawa daga cikinsu ba sa iya cin abinci.
kwalayen na dauke da rubutu kamar ‘Ka ceci rayuwarmu, Udom Emmanuel’, ‘Ka Biya mu hakkokinmu’, ’Muna jin yunwa’, da sauransu.
Anyi yunkurin jin ta bakin hukumomin da abin ya shafa amma abin ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan lokaci.