✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsintuwar kudi

Wani mutun ne talaka ya wayi gari ba kudi ba abinci, sai ya ce wa matarsa ta jira zai je kasuwa ya dawo. Da fitowarsa…

Wani mutun ne talaka ya wayi gari ba kudi ba abinci, sai ya ce wa matarsa ta jira zai je kasuwa ya dawo. Da fitowarsa kofar gida sai ya yi addu’a ya ce: ‘’Ya Allah Ka sa na tsinci Naira dubu biyu. Idan har Ka ba ni Naira dubu biyu, ni kuma zan ba da Naira dubu daya sadaka fisabilillahi.” Yana cikin tafiya har ya kusa zuwa kasuwa sai ga Naira dubu daya a kasa. Ya duka ya dauka cike da murna sai ya ce: “Oh, Allah gwani cikin ikonSa ka ga har Ya dauki nasa kason!”
Daga mai lamba 08091573703