✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tsintsiya Mdaurinki daya’

Taku; Amina Abdullahi Akwai wani dattijo, yana da yara da yawa kuma yana da dinbin arziki. Akwai abu daya da ke damunsa, abin shi ne.…

Taku; Amina Abdullahi

Akwai wani dattijo, yana da yara da yawa kuma yana da dinbin arziki. Akwai abu daya da ke damunsa, abin shi ne. yaran nasa ba su da hadin kai kullum suna cikin fada da juna, shi kuma yana tsoron barinsu a hakan, domin yana ganin cewa za su iya kashe junansu domin gadon da zai bar musu.

Ran nan ya kwanta jinya. Sai ya dauki tsinken tsintsiya daya ya mika wa babban dansa, ya bukaci ya karya. Ganin hakan sai abin ya ba dan dariya. Ya karya cikin sauki ba tare da wata matsala ba.

Sai ya dauko tarin tsintsiya a kulle, ya ce da dan nasa ya karya. Sai dan ya yi ya karya amma ya gagara, sai ya ce da ‘yayansa” idan kuka hada kanku babu wanda zai shiga tsakaninku don haka ku zama tsintsiya madaurinki daya “.  Daga nan sai yaran suka yafe wa juna, suka hada kansu.

Da fatan Manyan Gobe za su tsayawa’ yan uwansu a kodayaushe domin yin hakan na hana makiya cin nasara a kanku.